Puyol da Xavi sun samu rauni

Xavi
Image caption Xavi

'Yan Barcelona biyu, Carles Puyol da Xavi sun samu rani a wasan da kungiyarsu ta buga da Racing Santander a karshen mako.

Akwai shakku cewar 'yan wasan biyu ba za su samu bugawa Spaniya kwallo ba a mako mai zuwa.

Spaniya za ta buga wasa share fage na taka leda a gasar cin kofin Turai ne da kungiyar Liechtenstein, kafin kuma ta buga wasan sada zumunci da Argentina.

An dai sauya Xavi bayan da aka tafi hutun rabin lokaci, saboda raunin da ya samu kafar hagunsa.

Puyol dai bai samu buga wasan ba, saboda ya samu raunin ne a lokacin da ake motsa jiki kafin a fara wasan.