Christiano Ronaldo zai yi jinya ta makwanni uku

Ronaldo
Image caption Christiano Ronaldo ba haskaka ba a Afrika ta Kudu

Dan kwallon Portugal da Real Madrid Christiano Ronaldo akwai alamun ba zai taka leda na tsawon makwanni uku ba saboda raunin daya samu a idon sawu.

Ronaldo ya jimu a wasan da Real Madrid ta buga ranar lahadi tsakaninta da Real Mallorca inda aka tashi babu ci.

Wannan raunin na nufin cewar dan kwallon ba zai takawa Portugal leda ba a wasan ta Cyprus da kuma Norway na share fagen buga gasar cin kofin kasashen Turai.

Sanarwar da adreshin yanar gizon Real Madrid ta fitar ya ce" hoton idon sawunshi na dama ya nuna cewar zai shafe akalla makwanni uku kafin ya murmure".

Akwai yiwuwar Ronaldo din ba zai buga wasanni La liga biyu masu zuwa ba da kuma wasan farko na gasar Zakarun Turai tsakanin kungiyarsu da Ajax a ranar 15 ga watan Satunba.