Asamoah Gyan ya koma Sunderland

Gyan
Image caption Kwallon da Gyan ya zira itace ta fidda Amurka a gasar cin kofin duniya

Dan kwallon Ghana wanda ke taka leda a kungiyar Rennes Asamoah Gyan ya koma kungiyar Sunderland ta Ingila akan Euro miliyan 16.

Gyan me shekaru 24 a ranar litinin ya je London don tattaunawa da darektan Sunderland akan batun kulla yarjejeniya ta shekaru hudu.

Tuni kocin Rennes Frederic Antonetti ya bayyana cewar Gyan zai bar kungiyar don komawa Ingila.

Gyan na daga cikin 'yan kwallon da suka haskaka a Afrika ta Kudu inda ya zira kwallaye uku, amma kuma sai ya zubar da penariti tsakanin Ghana da Uruguay abinda kuma ya hana Black Stars din tsallakewa zuwa zagayen kusada karshe.