Ballack zai cigaba da zama kaptin din Jamus

Ballack
Image caption Lokacin da Kevin Boateng ya taka Micheal Ballack a idon sawu

Micheal Ballack zai cigaba da kasancewa kaptin din Jamus idan ya murmure daga raunin da yake fama dashi a idon sawunshi.

Hakan ya kawo karshen cacar baka tsakanin Ballack da Philipp Lahm wanda ya saka kambun kaptin din Jamus a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Dan shekaru 33, Ballack ya takawa Jamus leda a wasanni 98 inda ya zira kwallaye 42, kuma zia cigaba da saka kambum kaptin din kasarshi idan har ya warke daga raunin daya samu a wasan karshe na gasar cin kofin FA na Ingila tare da tsohuwar kungiyarshi Chelsea.

Shi dai Philipp Lahm wanda ya maye gurbin matsayin Ballack ya ce yanason ya cigaba da zama kaptin din koda Ballack ya dawo.

Akan haka ne sai Ballack din da Lahm suka yita musayar kalamai akan batun.

Kocin Jamus Joachim Loew a ranar Laraba yace"a 'yan kwanakin da suka wuce na tattaunawa da Ballack kuma na yanke shawara Micheal Ballack zai cigaba da kasancewa kaptin din kasarmu".

A halin yanzu dai Ballack din ya kulla sabuwar yarjejeniya tsakaninshi da Bayer Leverkusen.