Etuhu ya fasa bugawa Najeriya kwallo

Etuhu
Image caption Dan kwallon Najeriya Dickson Etuhu

Dan kwallon Fulham Dickson Etuhu ya fita daga cikin jerin 'yan kwallon da zasu bugawa Najeriya kwallo a wasan share fage na neman cancantar buga gasar cin kofin kwallon Afrika tsakaninta da Madagascar.

Etuhu ya fasa buga wasan ne saboda raunin daya samu a idon sawunshi a wasanshi na karshe a gasar premier a karshen mako.

Kakakin hukumar kwallon Najeriya NFF Robinson Okosun yace hukumar da umurci Etuhu ya bayyanawa likiti ainihin abinda ke damunshi.

Dan kwallon FC Brugge na Belgium Joseph Akpala ne ya fara cewar ba zai buga wasan ba saboda ciwon gwiwa.

Najeriya za ta dauki bakuncin Madagascar a ranar Lahadi a Calabar a wasan share fagen na rukunin B, wanda ya kunshi hadda Guinea da Ethiopia.