Rio Ferdinand zai dawo taka leda a Manchester

Ferdinand
Image caption Rauni ne ya hana Rio Ferdinand zuwa Afrika ta Kudu

Ana saran dan kwallon baya na Manchester United Rio Ferdinand ya koma taka leda a ranar Laraba bayan ya shafe watanni yana jinya.

Dan shekaru talatin da daya haihuwa, Ferdinand ya jimu ne bayan ya yi taho mu gama tsakaninshi da Emile Heskey lokacin horo, abinda ya haddasa bai je gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu ba.

Haka zalika, a ranar goma sha daya ga watan Satunba Ferdinand din za a fara wasa dashi a zubin farko a wasan United da Everton.

Kuma duk a wannan makon ne United din zata dauki bakuncin Rangers da Liverpool.

Bayaga Ferdinand sauran 'yan kwallon United Wes Brown da Anderson da Federico Macheda duk suma ana saran zasu dawo fagen tamaula.