UEFA ta hana amfani da Vuvuzela a Turai

Kakakin Vuvuzela
Image caption Kakakin Vuvuzela

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai, wato UEFA ta hana amfani da kakakin vuvuzela a duk gasa a Turai, kama daga wasanni share fage na cin kofin Turai da gasar zakarun Turai da kuma Europa.

Hukumar ta UEFA ta ce kakakin wanda aka yi amfani da shi a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu ba zai yi tasiri ba a Turai.

A cikin wata sanarwa da ta fitar Hukumar ta ce: " Amfani da kakakin vuvuzela al'ada ce ta nahiyar Afrika ba Turai ba, ba zamu bari a ci gaba da amfani da kakakin a Turai ba , saboda zai rika sa kara da zai damu jama'a, wanda kuma mutane a Turai ba su cika son kara ba".

Sanarwar ta kara da cewa karar kakakin ba zai sa 'yan kallo su ji dadin wasa ba, domin zai rika dauke musu hankali.