Tottenham ta sayi Van der Vaart daga Real Madrid

Van der Vaart
Image caption Dan kwallon Holland Rafael Van der Vaart

Tottenham Hotspurs ta sayi dan kwallon Real Madrid Rafael Van der Vaart akan pan miliyan takwas.

Gabda rufe kasuwar musayar 'yan kwallo a ranar talata ne Spurs din ta nuna aniyar sayen Van der Vaart me shekaru ashirin da bakwai da haihuwa.

Rafael Van der Vaart na daga cikin 'yan kwallon da suka takawa Holland leda a Afrika ta Kudu inda kasar ta samu kyautar azurfa.

Kafin kulla yarjejeniyar, sai da Spurs ta nemi izinin hukumar gasar premier ta Ingila don tabbatar da cewar bata saba ka'idar ciniki tsakaninta da Real Madrid.