Robinho da Ibrahimovic barazana ne ga Inter Milan-Mourinho

Mourinho
Image caption Kocin Real Madrid Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce cefenen 'yan kwallon da AC Milan tayi, babbar barazana ce ga Inter Milan a kokarin lashe gasar serie A.

Mourinho wanda ake kira 'Special One' ya ce yanasaran Inter ta cigaba da yin kakagidan data saba a Italiya, amma dai zuwa Zlatan Ibrahimovic da Robinho zai iya kawo cikas.

Ya shaidawa jaridar La Gazette dello cewar "AC Milan ta canza sosai saboda zuwa Robinho da Ibrahimovic".

Mourinho din dai ya bayyana cewar baya nadamar barin Inter Milan don komawa Real Madrid.