An dakatar da Kocin Portugal Queiroz na watanni shida

Queiroz
Image caption Kocin Portugal Carlos Queiroz tare da Christiano Ronaldo a Afrika ta Kudu

Hukumar dake kula da hana shan kwayoyi a tsakanin 'yan kwallo a Portugal ta dakatar da mai horadda 'yan kwallon kasar Carlos Queiroz na watanni shida.

Matakin hukumar ya biyo bayan zagin da Queiroz ya yiwa daya daga cikin jami'anta.

Sai dai rahotanni sun nuna cewar Carlos Queiroz din zai daukaka kara a gaban kotun sauraron laifukan wasanni. A lokacin shirye shiryen gasar cin kofin duniya da akayi a Afrika ta kudu ne Queiroz din ya zagi wani jami'i a kokarinshi na gwada 'yan kwallon don tabbatar da cewar basu sha haramtattun kwayoyi ba.

Abinda wannan hukuncin ke nufi shine Queiroz ba zai jagoranci wasanni hudu na share fage ba da Portugal za ta buga.

A watan Yulin shekara ta 2008 ne Queiroz ya kulla yarjejeniya da Portugal har zuwa shekara ta 2012.