Bolton ta kori dan Najeriya Danny Shittu

Shittu
Image caption Danny Shittu na neman kungiyar da ze takawa leda a Turai

Kungiyar Bolton Wanderers ta soke kwangila tsakaninta da dan kwallon Najeriya Danny Shittu.

Dan shekaru talatin da haihuwa, Shittu ya kulla yarjejeniya ta shekaru uku da Bolton daga kungiyar Watford akan pan miliyan biyu a watan Agustan shekara ta 2008.

A kakar wasanshi na farko a Bolton ya taka leda ne sau 12, sannan kuma a kakar wasan data wuce ba a taba fara wasa dashi ba.

Amma duk da haka da kwallon ya bugawa Najeriya duka wasanninta uku a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.