Beckham zai dawo taka leda

David Beckham
Image caption David Beckham

Tsohon kyaftin din Ingila David Beckham ya ce yana fatar taka leda a wasan da kungiyarshi ta LA Galaxy za ta buga da Columbus Crew a ranar 11 ga watan Satumba.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 35 yana murmurewa ne bayan ya turgude kafarsa a lokacin da yake takawa AC Milan leda na wucin gadi a kakar wasan bara.

An dai hasashen cewar dan wasan zai dawo taka leda ne ranar daya ga watan Okutoba.

Beckham, wanda ya bugawa Ingila wasanni 115 bai samu taka leda ba a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu saboda raunin da ya samu.

A baya-baya nan dai kocin Ingila Fabio Capello ya ce ba zai kira dan wasan kuma ba , saboda shekarushi sun hau.