Faransa ta sallami Raymond Domenech

domenech
Image caption Raymond Domenech a lokacin da yaki gaisawa da Carlos Alberto

Hukumar kwallon Faransa ta sallami tsohon kocin kasar Raymond Domenech wanda ta sauya shi bayan gasar cin kofin duniya.

Hukumar duk da cewar ta nada Laurent Blanc a matsayin koci, amma dai ta cigaba da biyan Domenech albashi bayan mummunar rawar da Faransa ta taka a Afrika ta Kudu.

Rahotanni sun nuna cewar an kore shine saboda rashin iya gudanar da aiki a matsayinshi na mai horadda 'yan kwallon Faransa a Afrika ta Kudu.

Domenech ya sha suka a sosai sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakaninshi da 'yan kwallon Faransa har aka kori Nicolas Anelka sannan kuma sauran 'yan kwallon suka yi zanga zanga.

Bugu da kari an zargeshi da rashin nuna dattaku a wasan Faransa da Afrika ta Kudu inda yaki gaisawa da kocin Bafana Bafana Carlos Alberto Parreira saboda an doke Faransa daci biyu da daya.

Bayan gasar cin kofin duniya, hukumar kwallon Faransa ta dakatar da Nicolas Anelka da Patrice Evra da Franck Ribery da Jeremy Toulalan saboda rawar da suka taka a hatsaniyar.