Najeriya ta doke Madagascar daci biyu da nema

Super Eagles
Image caption Tawagar 'yan kwallon Super Eagles

Najeriya ta samu galaba akan kasar Madagascar daci biyu da nema a wasan neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a shekara ta 2012.

Dan kwallon Rubin Kazan Martins Obafemi ne ya fara cin kwallon sannan Eneramo yaci na biyun tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sannan bayan an dawo hutun rabin lokacin Najeriya dai bata cigaba da haskakawa ba kamar yadda tayi a zubin farko, amma dai Martins ya kara cin kwallo sai alkalin wasa yace yayi satan gola.

Sakamakon wasu wasannin da aka buga:

Morocco 0 - 0 Central Africa Ethiopia 1 - 4 Guinea Mozambique 0 - 0 Libya Zambia 4 - 0 Comoros Swaziland 0 - 3 Ghana