Manchester United ta cire Hargreaves ta saka Bebe

Bebe
Image caption Manchester United ta sayi Bebe akan fiye da pan miliyan bakwai

Sabon dan kwallon Manchester United Bebe ya shiga cikin jerin 'yan kwallo 25 da kungiyar ta saka don buga gasar cin kofin zakarun Turai,amma ba a saka Owen Hargreaves ba.

Da farko an dauka Bebe wanda dan kasar Portugal ne baya cikin jerin, amma sai hukumar UEFA ta tabbatar da cewar yana ciki.

Sai dai Hargreaves me shekaru 29 sau daya tal ya bugawa United kwallo a gasar zakarun Turai cikin shekaru biyun da suka wuce saboda raunin da yake fama dashi.

Amma dai an saka sunayen Hargreaves da Bebe cikin 'yan kwallon Manchester United 25 a gasar Premier.