Kotu ta soke zaben shugaban NFF Aminu Maigari

Maigari
Image caption Ta leko ta koma,murna ta koma ciki a wajen Aminu Maigari

Wata babbar kotun Tarayya dake Lagos ta soke zaben shugabannin Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Nijeriya, NFF.

Kotun ta ce da ma ta bada umarnin kada a gudanar da zaben, amma Hukumar ta NFF ta yi gaban kanta ta gudanar da shi saboda haka ta ce zaben haramtacce ne.

Zaben da aka gudanar a makon da ya gabata an zabi Alhaji Aminu Maigari a matsayin shugaba.

Tun kafin zaben dai daya daga cikin 'yan takarar kujerar shugaban NFF, Segun Odegbami ya shigar da kara cewar an saba ka'idoji kuma an tafka kura kurai a shirye shiryen zaben.

Kotun ta kuma bada umarnin a sake yin wani sabon zaben fil.