Dickson Etuhu ya sabunta yarjejeniyarshi a Fulham

Etuhu
Image caption Dickson Etuhu yana gurmuzu da Tim Cahill na Everton

Dan kwallon Najeriya Dickson Etuhu ya kara kulla sabuwar yarjejeniya da Fulham na shekaru uku masu zuwa.

Dan shekaru ashirin da takwas, Etuhu zai cigaba da taka leda a Cottage har zuwa shekara ta 2014, kuma sanya hannun a wannan yarjejeniyar ya kawo karshen batu akan sake hadewa da Roy Hodgson a Liverpool.

Dan kwallon Super Eagles din ya koma Fulham ne daga Sunderland a watan Agustan 2008 kuma sun fahimci juna da Danny Murphy a tsakiyar Fulham.

Etuhu ya fara taka leda ne a Manchester City, kuma yana cikin tawagar data kai wasan karshe na gasar Europa da kuma 'yan kwallon Najeriya da suka je Afrika ta Kudu don buga gasar cin kofin duniya.