NFF:Ana zargin Sani Lulu da wasu uku akan naira biliyan daya

Sani Lulu
Image caption An tsige Sani Lulu daga mukamin shigaban NFF bayan gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu

An gurfanar da wasu tsaffin shugabanin hukumar kula da kwallo kafa a Najeriya wato NFF bisa zargin sama da fadi da dala miliyan takwas wato naira biliyan daya da dubu dari biyu na kudaden gasar cin kofin duniya da aka yi a Afrika ta Kudu.

Mutane hudun sun hada da tsohon shugaban NFF Sani Lulu Abdullahi da Bolaji Ojo-Oba da Taiwo Ogunjobi da Amanze Uchegbulam wadanda suka bayyana gaban babbar kotu a Abuja.

Dama dai tuni aka koresu duka saboda mummunar rawar da Najeriya ta taka a gasar cin kofin duniya.

Kakakin hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC Femi Babafemi ya shaidawa BBC cewar ana tuhumar mutanen hudu akan kashe dala miliyan dari takwas akan tawagar data je Afrika ta Kudu inda su Sani Lulu suka ce mutane 220 ne suka je alhalin mutane 49 ne.

Har wa yau sun kashe dala dubu dari hudu wajen shirya wasan sada zumunci tsakanin Super Eagles da Columbia a London sannan kuma anci tarar Najeriya dala dubu dari da ashirin da biyar saboda saba yarjejeniya da wani Otal a Afrika ta Kudu.