Argentina ta lallasa Spain a wasan sada zumunci

Lionel Messi
Image caption Lionel Messi na murnar zura kwallo

Mai rike da kambun gasar cin kofin duniya, wato Spaniya ta sha kashi a hannun a Argentina da ci hudu da guda.

Dan kwallon duniya Lionel Messi ya karawa sauran abokan wasansa kwarin gwiwa bayan da ya zura kwallon farko ana minti tara da fara wasan.

Gonzalo Higuain ne ya zura ta biyu bayan minti uku da Messi ya zura kwallon farko sannan kuma Carlos Tevez ya zura ta uku ana minti 34 da wasan.

An dai tafi hutun rabin lokaci ne Argentina na cin Spain kwallaye uku da nema.

Spain dai ta samu farke kwallo guda ne ana sauran minti bakwai a kammala wasan, amma da aka shiga karin lokaci sai Sergio Aguero ya zura ta hudu a karin lokaci.

Wannan dai shine karo na farko da aka zurawa Spain kwallaye hudu a tsawon shekaru goma, kuma wannan shine wasa na uku cikin hamsin da takwas da aka doke kungiyar tun daga shekarar dubu biyu da shida.