Nadal zai buga wasan gab da kusa dana karshe a US Open

Rafeal Nadal
Image caption Rafeal Nadal

Rafael Nadal ya tsallake zuwa wasan gab da kusa dana karshe a gasae US Open bayan ya doke Feliciano Lopez.

Dan wasan Tennis din wanda shine na daya a duniya zai fafata ne da dan kasarsa, Fernando Verdasco.

Nadal ya ce yana da kwarin gwiwa zai lashe gasar ta US open

"ina kokari yadda nake wasa amma ina ganin bai ga yadda nake soba, amma a kullum idan nayi wasa ina kara kwazo." In ji Nadal