Beckham ya murmure ya komo fagen tamaula

Beckham
Image caption Kocin Ingila Fabio Capello ya ce Beckham ya tsufa

Dan Ingila David Beckham ya komo taka leda bayan shafe watanni shida yana jinya, inda a ranar Asabar ya shigo bayan hutun rabin lokaci a wasanda LA Galaxy ta doke Columbus daci uku da daya.

Tsohon kaptin din Ingilan mai shekaru 35, tun a watan Maris rabonshi da ya buga kwallo, raunin da ya hanashi zuwa gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Ana sauran minti ashirin a tashi wasan, Beckham ya shigo sannan daga bisani aka bashi katin gargadi saboda karawar da suka yi da Emmanuel Ekpo.

Beckham yace"Na ji dadin shawon kan matsalar, kuma yanzu garau nake".

Tsohon dan kwallon Manchester United da Real Madrid din ya jaddada aniyarshi ta sake bugawa Ingila kwallo duk da cewar Fabio Capello ya ce Beckham din ya tsufa da takawa Ingila leda.