Kim Clijsters ta lashe gasar US open

Clijsters
Image caption Kim Clijsters tare da 'yar ta bayan ta lashe gasar US open

'Yar Belgium Kim Clijsters ta kare kofinta na US open a gasar tennis bayan ta samu galaba akan Vera Zvonareva a gasar da aka buga a Flushing Meadow a New York.

'Yar shekaru ashirin da bakwai, Clijsters ta doke 'yar Rashar da seti biyu a jere.

Wannan nasarar ta nuna cewar Clijsters ta lashe manyan kofinanta na gasar tennis ne duk a New York inda ta lashe kofinta na farko a shekara ta 2005.

Clijsters tace"a gaskiya na ji dadin bana saboda na kare kofin dana lashe a bara".

A kara biyun da Clijsters tayi da Zvonareva a baya, duka Zvonareva ce ke samun galaba.