Fulham ta ci karo da karayar dan kwallonta Zamora

Zamora
Image caption Bobby Zamora a lokacin da ya karya kafa

Kungiyar Fulham ta Ingila za ta buga kwallo banda Bobby Zamora akalla na watanni hudu, bayan da dan kwallon ya karya kafa a wasan da suka doke Wolves daci biyu da daya.

An fitar da Zamora daga cikin filin minti 28 kacal da fara wasan bayan sunyi taho mu gama da Karl Henry.

A ranar Juma'ar data gabata ne dan shekaru taran ya sabunta yarjejeniyarshi da Fulham don cigaba da kasancewa da ita har zuwa shekara ta 2014, sannan ya bugawa Ingila wasanshi na farko a watan Agusta.

Kocin Fulham Mark Hughes yace"Ya karya kafanshi a dai dai saman idon sawunshi, kuma zai shafe akalla watanni hudu ya jinya".

Zamora ya kulla yarjejeniya da Fulham daga West Ham a watan Yulin 2008 sannan a kakar wasan data wuce ya zira kwallaye 19 a gasar premier.