Real Madrid za ta rufe saman Santiago Bernabeu

Perez
Image caption Shugaban Real Madrid Florentino Perez

Shugaban kungiyar Real Madrid Florentino Perez ya bayyana cewar akwai shirin rufe saman filin wasansu wato Santiago Bernabeu dake tsakiyar babban birnin Spain.

Real wacce ta lashe gasar zakarun Turai sau tara na kokarin saka rufi a filin wasan da aka gina a shekarar 1947.

Wata jaridar jikin gida ta ambato Perez na cewar"zamu yiwa filin wasanmu garan bawul don cigaba da shiga gaban sauran kungiyoyi".

Sai dai Perez bai bayyana lokacin da za a yiwa filin wasan kwaskwarima ba. Filin wasan dai an saka mashi sunan tsohon shugaban Real ne, kuma yanzu yana daukar mutane akalla dubu tamanin a yayinda kusan mutane dubu dari bakwai kan zuwa yawon bude ido duk shekara.