Rooney zai buga wasan Manchester United da Rangers

Rooney
Image caption Rooney ne yafi zira kwallo a United a bara

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney ya shiga cikin horo da sauran 'yan kwallo a ranar litinin da safe a shirye shiryen tun karar Rangers a wasan gasar zakarun Turai a ranar Talata.

Rooney bai taka leda ba a wasansu da Everton saboda Sir Alex Ferguson ya ce baison 'yan kallo su zagi dan kwallon.

Wata jarida ta buga labarin cewar Rooney ya biya wata mace mai zaman kanta donsu tara.

A halin yanzu dai Chelsea ta fi Manchester da maki hudu a gasar premier.

Kuma a gasar zakarun Turai, United din na rukunin guda ne da Valencia da Bursaspor na kasar Turkiya.