Ghana na zawarcin sabon kocin Black Stars

Rajevac
Image caption Milovan Rajevac ya koma Saudi Arabiya inda zai karbi makudan kudade

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Ghana GFA za ta tattauna a ranar Litinin don yanke shawara akan daukar hayar sabon mai horadda 'yan kwallon kasar bayan Milovan Rajevac yaki amincewa ya cigaba da zama.

A baya hukumar kwallon Ghanar ta saran Rajevac zai kara zama na tsawon shekaru hudu amma sai yaki ya koma Saudi Arabiya inda zaifi samun kudi.

Hukumar GFA dole ne ta nada sabon koci nanda wata guda saboda Black Stars din za ta kara da Sudan a wasan share fage na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika.

Shugaban GFA Kwasi Nyantakyi ya shaidawa BBC cewar za ayi taron gaggawa don yanke hukunci akan tsarin daukar hayar sabon koci.

Milovan Rajevac wanda dan kasar Serbia ne ya kama aiki da Black Stars a watan Agustan 2008 bayan ficewar Claude Le Roy.

Kuma Rajevac din ya jagoranci Black Stars zuwa wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a Angola a bana da kuma zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.