UEFA:Rauni zai hana 'yan kwallon Arsenal taka leda

Wenger
Image caption Arsene Wenger a cikin funshi bayan an doke Arsenal

Kungiyar Arsenal ta Ingila za ta kara da kungiyar Braga ta Portugal a gasar zakarun Turai a ranar Laraba ba tare da 'yan kwallonta Thomas Vermaelen da Abou Diaby.

Vermaelin na fama da ciwon cinya ne a yayinda Diaby ya jimu a idon sawunshi.

Sai dai Samir Nasri ya murmure daga ciwon gwiwa a yayinda Gael Clichy da Bacary Sagna ake saran zasu buga bayan an ajiyesu su huta a wasan Arsenal da Bolton a ranar Asabar data wuce.

Har ya wau Theo Walcott da Robin van Persie duk suna da ciwo a idon sawunsu, kamar yadda rauni zai hana Nicklas Bendtner da Aaron Ramsey taka leda.