FIFA ta ci tarar dan kwallon Algeriya Rafik Saifi

Algeriya
Image caption Tawagar 'yan kwallon Algeriya

Hukumar dake kula kwallon kafa ta duniya FIFA ta ci tarar dan kwallon Algeriya Rafik Saifi Euro dubu biyu da dari uku.

Hukuncin na FIFA ya biyo bayan marin wata 'yar jarida bayan kamalla wasan Algeriya da Amurka a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Saifi ya mari Asma Halimi 'yar jaridar dake aiki da daily Competition ta Algeriya a wajen hira da 'yan kwallon bayan da Amurka ta doke Algeriya daci daya me ban haushi.

Haili a baya ta yi rubutu akan Saifi kafin wannan abun ya faru, sannan kuma ta rama marinne kafin ta kaiwa FIFA kara.