UEFA: Arsenal ta lallasa Sporting Praga daci shida da nema

Fabregas
Image caption Cesc Fabregas ya zira kwallaye biyu a ragar Spraga

Sabanin yadda kungiyoyin gasar premier ta Ingila suka kasa taka rawar gani a yammacin talata, a wannan karon dai wato a wasannin yammacin laraba, Arsenal da Chelsea ligi ligi suka yiwa abokan karawarsu.

Ita dai Arsenal casa Sporting Praga tayi daci shida da nema a filinta na Emirates, inda Fabregas yaci biyu sannan Carlos Vela shima yaci biyu sai Arshavin da Chamakh wadanda suka ci guda guda.

Zakaran gasar premier wato Chelsea kama kungiyar Zilina ta yi can a Slovakia kuma kwallaye hudu Chelsea din ta zira a yayinda Zilina din ta zira guda.

Sakamakon wasannin da aka kara:

*AC Milan2-0Auxerre *Arsenal6-0Braga *Bayern Munich2-0Roma *CFR Cluj-Napoca2-1Basle *Marseille0-1Spartak Moscow *MSK Zilina1-4Chelsea *Real Madrid2-0Ajax *S. Donetsk1-0Partizan Belgrade