Antonio Valencia ya karye a idon sawunshi

Valencia
Image caption An dauki Antonio Valencia ranga ranga ne daga cikin fili

Dan kwallon Manchester United Antonio Valencia watakila ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana bayan ya jimu a idon sawunshi a wasansu da Rangers wanda aka tashi babu ci.

An dauki dan kwallon akan makara bayanda ya kara da Kirk Broadfoot na Rangers

Valencia mai shekaru 25 a yanzu haka yana asibiti kuma za a yi mashi tiyata a ranar Laraba.

Sir Alex Ferguson yace"abin kamar karaya da targade".

Ferguson ya kwatanta raunin da irin wanda tsohon dan kwallon United Alan Smith yaji inda ya karya kafarshi.