Sam Allardyce ya zargi Arsene Wenger

Wenger da Allardyce
Image caption Wenger da Allardyce sun dade suna takun saka

Kocin Blackburn Rovers Sam Allardyce ya zargi mai horadda 'yan kwallon Arsenal Arsene Wenger akan cewar Wenger din na amfani da kafafen yada labarai don kada alkalan wasa su daina daukar hukunci akan 'yan Arsenal.

Kocin Arsenal din yayi kakkausar suka akan 'yan kwallo saboda raunin da Abou Diaby ya ci a wasansu da Bolton a ranar Asabar.

Allardyce yace: "mutum ne me wayo, kuma yanasa alkalan wasa su canza shawara".

Allardyce da Wenger sun saba cacar baka akan salon yadda 'yan kwallonsu ke taka leda.