Carlo Ancelotti ya jinjinawa Nicolas Anelka

Anelka
Image caption Dan kwallon Chelsea Anelka

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce Nicolas Anelka shine kashin bayan nasarar da Chelsea ta samu akan MSK Zilina daci hudu da nema a wasan zakarun Turai.

Anelka a wasan ya zira kwallaye biyu sannan kuma ya baiwa Michael Essien shima yaci.

Ancelotti yace"Anelka ne sirrin nasarar, wasanshi yayi kyau sosai".

A kakar wasan ta bana dai har Chelsea ta zira kwallaye 21 cikin wasanni biyar.