Marcel Desailly na son ya zama kocin Ghana

Desailly
Image caption Tsohon dan kwallon Faransa Marcel Desailly

Tsohon kaptin din Faransa Marcel Desailly ya ce yanason ya zama kocin Ghana.

Dan shekaru arba'in da hudu wanda aka haifa a Ghana kuma iyayenshi 'yan kasar ne, ya ce yanason ya maye gurbin Milovan Rajevac wanda yayi murabus a matsayin kocin Black Stars.

Desailly ya bayyanawa wani gidan talabiji a Ghana mai suna Viasat cewar"a yanzu na shirya tsaf don zama kocin Black Stars".

A baya sau biyu Ghana na baiwa Desailly mukamin amma yana ki.

Tsohon dan kwallon AC Milan da Chelsea din baitaba zama koci ba, amma dai saboda irin rawar daya taka a matsayinshi na dan kwallo ana yawan alakanta shi da horradda 'yan kwallon Ghana a duk lokacin da kasar ta rasa koci.

Desailly na cikin tawagar Faransa wacce ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998 da kuma kofin kasashen Turai a shekara ta 2000.