Ba zan jagoranci Portugal ba-Mourinho

Mourinho
Image caption Jose Mourinho'the special one'

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce ba zai karbi mukamin wucin gadi na zama kocin Portugal ba.

An ambato Mourinho yana bayyana mamakinshi akan yadda kungiyar Madrid taki amincewa ya jagoranci tawagar 'yan kwallon kasarshi ta haihuwa a wasanni biyu duk da cewar a lokacin kungiyoyi a Turai suna hutu. Sai dai Darekta Janar na Real Madrid Jorge Valdano ya ce hukumar kwallon Portugal bata tuntubesu ba adon haka babu sauran magana akan batun.

Mourinho dai ya ce bai gane dalilan da suka sanya ba hukumar kwallon kasarshi wato Portugal taki tuntubar Real Madrid koda yake dai maganar ta wuce.

Rahotanni sun nuna cewar an nada Paulo Bento don ya jagoranci tawagar 'yan kwallon Portugal din.