Micheal Owen ba zai koma Aston Villa ba-Ferguson

Ferguson da Owen
Image caption Ba a barin Micheal Owen ya taka leda na minti casa'in

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce Gerard Houllier na bata lokacinshi ne wajen tunanin sayen Micheal Owen ya koma Aston Villa.

Houllier ya bayyana a farkon wannan makon cewar yanason ya kara aiki da Owen bayyan zaman da suka yi tare a Liverpool a wancan lokacin.

Saboda Owen baya taka leda sosai yasa wasu ke tunanin dan kwallon zai koma Villa Park a lokacin musayar 'yan kwallo a watan Junairun badi.

Ferguson ya ce ba zai saki Owen ba, kuma zai fara bashi damar taka leda sosai a kakar wasa ta bana.

Wasanni biyar kacal aka fara da Owen tun bayan zuwanshi Old Trafford a shekara ta 2009 sannan kuma sau uku kawai ya taka leda a kakar wasa ta bana.