CAF: Esperance za ta kara da Al Ahly a zagayen kusada karshe

Caf
Image caption Kofin da kungiyoyin Afrika ke takara akai

Zakarun gasar Tunisia Esperance za ta kara da Al Ahly ta Masar a wasan zagayen kusada karshe na gasar cin kofin zakarun kwallon Afrika.

Ita kuwa mai rike da kofin wato TP Mazembe ta kasar Congo za ta hadu ne da JS Kabylie ta Algeria a daya wasan zagayen kusada karshen da za a buga a wata mai zuwa.

Al Ahly ce ta zama ta farko a rukunin B a yayinda Kablylie ta zama ta biyu sai Ismaili da Heartland aka cire su daga takarar.

Esperance ta Tunisia ce ta karke ta farko a rukunin A sai kuma TP Mazembe ta zama ta biyu, inda aka fidda Dynamos ta Zimbabwe da Entente Setif.

Za a buga wasannin zagayen kusada karshen ne a watan Oktoba sai kuma wasan karshe da za ayi a karshen makon 12-14 na watan Nuwamba.