Dan kwallon Real Madrid Canales ya ji rauni

Canales
Image caption Sabon dan kwallon Real Madrid Sergio Canales

Da alamu sabon dan kwallon Real Madrid Sergio Canales zai yi jinya ta makwanni biyu zuwa uku saboda rauni a idon sawunshi.

Dan shekaru 19, dan kwallon ya jimu ne a lokacin horo a ranar Lahadi ba tare da wani dan kwallo ya taba shi ba.

Jaridar Sports daily Marca ta wallafa cewar za ayi wa Canales gwaje gwaje don gannin irin tsananin raunin.

Idan aka tabbatar, Canales wanda ya koma Real daga kungiyar Racing Club Santander a ranar daya ga watan Yuli, ba zai buga wasan Real da Auxerre a ranar 28 ga watan Satumba na gasar zakarun Turai.

Tunda aka fara kakar wasa ta bana dai babu kungiyar data doke Real Madrid karkashin jagorancin Jose Mourinho.