Messi zai shafe makwanni biyu yana jinyar idon sawunshi

Messi
Image caption Lionel Messi a lokacin da aka fiddashi a cikin fili

Gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi ba zai taka leda ba a wasanni biyu saboda rauni a idon sawunchi daya samu a wasan da Barca ta doke Athletico Madrid daci biyu da daya.

Dan kasar Argentina din an fiddashi ne bayan hutun rabin lokaci bayan sun gwabza da dan kwallon Athletico Tomas Ujfalusi.

Sakamakon wannan raunin dai, Messi ba zai buga wasan Barca da Sporting Gijon da Athletic Bilbao.

Har wa yau Barcelona za ta kara da Rubin Kazan a gasar zakarun Turai a ranar 29 ga watan Satumba. A lokacin da Ujfalusi suka gwabza da Messi din dai, alkalin wasan ya bashi jan kati sannan kuma kocin Barca Pep Guardiola ya fusata akan batun.

Guardiola yace"mun ji dadin samun nasara amma muna bakin cikin raunin Messi".