Sierra Leone ta gayyaci Nigel Reo-Coker daga Aston Villa

Reo Coker
Image caption An haifi Reo Coker ne a Ingila amma iyayenshi 'yan Sierra Leone

Sierra Leone ta gayyaci dan kwallon Aston Villa Nigel Reo-Coker a karon farko don ya taka mata leda.

BBC ta fahimci cewar kocin Leone Stars din Christian Cole zai gayyaci dan shekaru 26 a wasansu da Afrika ta Kudu na neman cancantar buga gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a 2012.

Reo-Coker dai a Ingila aka haifeshi amma dai iyayenshi 'yan kasar Sierra Leone ne.

Har wa yau ya yi kaptin din 'yan kwallon Ingila 'yan kasada shekaru 21 amma dai bai bugawa babbar tawagar 'yan kwallon Ingila ba.

A cewar sakatare janar na hukumar kwallon Sierra Leone AbdulRahman Swarray ya ce baida shakkun cewar dan kwallon zai sauya sheka.