Hukumar FA na tuhumar Wenger akan zagin alkalin wasa

Wenger
Image caption Arsene Wenger ya fusata da aka farke kwallon

Hukumar dake kula gasar premier ta Ingila wato FA na tuhumar kocin Arsenal Arsene Wenger saboda aikata ba dai dai ba a karshen wasan da Arsenal ta tashi kunen doki tsakaninta da Sunderland.

Anga Wenger ya yi gaba da gaba da alkalin wasa Martin Atkinson bayan da Darren Bent ya farke kwallo a cikin minti na biyar a karin lokaci.

Atkinson dai ya daga allon dake nuna cewar an kara minti hudu amma dai sai gashi an farke kwallo bayan minti hudun ya wuce da dakika 15.

Wenger nada dama daga nan zuwa ranar 23 ga watan Satumba na ya amince da tuhumar ko kuma yaki amincewa.

Idan har ya amsa laifin,za a dakatar dashi na wasa guda sannan kuma aci tararshi pan dubu takwas.