AWC: Afrika ta Kudu na rukunin guda da Najeriya

Kofin AWC
Image caption 'Yan kwallon mata na Afrika zasu yi takara akan wannan kofin

Mai masaukin baki Afrika ta Kudu za ta hadu da Tanzaniya a wasan farko na gasar cin kofin kwallo na matan Afrika da za a fara a wata mai zuwa.

Sauran kasashen dake rukunin farkon sune Mali da Najeriya.

A rukunin na biyu kuwa akwai kasashen Equatorial Guinea da Ghana da Kamaru da kuma Algeriya.

Za a fara gasar ne daga ranar 29 ga watan Oktoba zuwa 14 Nuwamba a yayinda kasashen da suka zo na farko dana na biyu zasu wakilci Afrika a gasar cin kofin duniya ta mata a Jamus a badi.

Rukunin A Afrika ta Kudu (mai masaukin baki) Tanzaniya Najeriya Mali

Rukunin B Equatorial Guinea (mai rike da kofin) Kamaru Algeriya Ghana