Cesc Fabregas zai yi jinya ta makwanni uku

Fabregas
Image caption Cesc Fabregas ya cika 'laulayi'

Kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas zai shafe makwanni uku yana jinya bayan ya raunata kafadarshi.

Fabregas me shekaru 23 ya fita yana dingishi a wasan da Arsenal ta tashi kunen doki tsakaninta da Sunderland.

Wata sanarwa da Arsenal ta fitar a yanar gizonta ta ce" Mun tabbatar da cewa Cesc Fabregas zai yi jinya ta makwanni biyu zuwa uku".

A ranar litinin ne aka dauki hoton raunin aka tabbatar da haka.

Fabregas ba zai taka leda a wasan Carling na ranar Talata tsakaninsu da Tottenham da kuma wasan zakarun Turai tsakanin Arsenal da Partizan Belgrade sai kuma na gasar premier da West Brom.

Har wa yau akwai shakkun watakila ba zai buga wasan Arsenal da Chelsea a ranar uku ga watan Oktoba da kuma wasa Spain tsakaninta da Lithuania a ranar takwas ga watan.