Bayern na bukatar Euro miliyan daya daga Holland akan Robben

Robben
Image caption Arjen Robben a lokacin da cinyarshi ta rike

Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya baiwa hukumar kwallon kasar Holland wa'adi ta biya su Euro miliyan daya saboda raunin Arjen Robben.

Koda yake Holland ta sha kashi a wajen Spain a wasan karshe na gasar cin kofin duniya daci daya me ban haushi, amma dai Bayern na takaicin cewar wasanne ya janyo ciwon Robben ya tsananta abinda kuma ya sanya watakila sai a watan Junairun badi zai cigaba da taka leda.

Rummenigge ya bayyana cewar rashin Robben babbar cikas ce gare su, a don haka suna bukatar kudin ba dadewa ba.

Rummenigge ya kara da cewar matakinsu na gaba shine sukai batun gaban FIFA don sasanta lamarin.