Arsenal ta samu riba mai tsoka

Tsohon filin wasa na Highbury
Image caption Tsohon filin wasa na Highbury ya taimakawa tattalin arzikin Arsenal

Kungiyar Arsenal ta bayyana cewa ta samu riba mai tsoka wacce adadinta yakai pan miliyan 56, kafin ta biya haraji.

Kungiyar har ila yau ta ce ta biya dukkan basukan da ake binta kan rukunin gidajen data gina a tsohon filin wasanta na Highbury. Alkaluman wadanda suka faro daga farkon shekara zuwa watan Mayun bana, sun nuna cewa adadin ya tashi daga pan miliyan 10 da rabi idan aka kwatanta da watanni 12 da suka gabata.

Shugaban kungiyar ta Arsenal Ivan Gazidis yace: " Kungiyar ta samu ci gaba sosai a shekarar data gabata.: Arsenal tace ta sayarda gidaje 362 a rukunin gidaje na Highbury, inda filin wasanta na da yake.