Rooney na cikin damuwa: Ferguson

Wayne Rooney da Ferguson
Bayanan hoto,

Rooney na da mahimmanci sosai ga Manchester United

Kociyan Manchester United Sir Alex Ferguson, ya ce Wayne Rooney na cikin damuwa da takura sakamakon matsin lambar da yake fuskanta abisa al'amuran da suka shafi dangantakarsa da iyalinsa. Rooney, dan shekaru 24, ya ja hankalin jama'a bayan da aka zarge shi da amfani da matan banza alhalin yana da iyali.

Kuma tun wannan lokacin, kwallo daya kawai ya zira a wasanni hudu da ya buga a kakar wasanni ta bana.

"A ganina Rooney yana da kwarin guiwa," kamar yadda Ferguson ya shaidawa jaridar Gazzetta dello Sport ta kasar Italiya.

"Sai dai a zahiri take cewa ya cikin matsin lamba a kokari fuskantar irin abinda yafi dacewa ya maida hankali akai a matsayinsa na dan adam."

Rooney ya zira kwallaye 34 a kakar wasanni ta bara, sai dai bai taka rawar gani a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Afrika ta Kudu ba.