An nada Tom Saintfiet a matsayin kocin Zimbabwe

Saintfiet
Image caption Kocin Zimbabwe Tom Saintfeit

An nada Tom Saintfiet a matsayin kocin Zimbabwe duk da cewar yana da sauran wa'adi a tawagar kwallon Namibia.

Dan kasar Belgium din ya shafe kwanaki hudu a Zimbabwe kafin a bashi mukamin saboda rarrabuwar kawuna a hukumar kwallon kasar Zimbabwe (Zifa).

Jama'a da dama sun nemi kocin riko Norman Mapeza a bashi mukamin na dundundun.

A Zifa technical committee recommended Saintfiet despite his Namibia links.

Amma duk da irin kiraye kiraye da kuma korafi akanshi, shugaban Zifa Cuthbert Dube ya nada Saintfiet.