Brazil za ta hadu da Iran a wasan sada zumunci

Brazil
Image caption Tutar kasar Brazil

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Brazil ta ce 'yan kwallon Samba din zasu kara da Iran a wasan sada zumunci a ranar bakwai ga wata mai zuwa a Abu Dhabi.

Kakakin hukumar Rodrigo Paiva ya ce zasu sanya hannu akan yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu.

Paiva ya bayyana a ranar Litinin cewar bayan karawar Brazil da Iran,Brazil din zata kara da wata kasar a ranar 11 ga watan Oktoba a birnin London.

Image caption Tutar Iran

A baya bayannan Brazil ta fuskanci cikas a fagen kwallon kafa a duniya ,tun bayan da Holland ta fidda ta a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a zagayen gabda na kusada karshe.

Bayan gasar a Afrika ta Kudu, sai aka kori mai horadda 'yan kwallon kasar Carlos Dunga tare da sauran mataimakanshi.