UEFA:Rooney ya jimu a idon sawunshi

Rooney
Image caption wayne Rooney na cikin rudu

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney ba zai buga wasan zakarun Turai ba tsakaninsu da Valencia a ranar Laraba saboda rauni a idon sawunshi.

Rooney yaji raunin ne a wasan da aka tashi biyu da biyu tsakaninsu da Bolton a ranar Lahadi inda aka canja shi a minti na 61 a filin wasa na Reebok.

Kocin United Sir Alex Ferguson ya shaidawa manutd.com a ranar Litinin cewar a ranar Litinin cewar dan shekaru 24 ba zai tafi Spain dasu ba a ranar Talata kafin wasan na Laraba.

Rooney dai ya shiga cikin matsala ne bayan da wata jarida ta wallafa cewar yana mu'amala da matan banza.