Europa:Liverpool ta ajiye Steven Gerarrd ya huta

Steven Gerrard
Image caption Steven Gerrard yana godiya ga 'yan kallo

Kaptin din Liverpool Steven Gerrard ba zaiyi tafiya tare da sauran tawagar kungiyar ba don fafatawa a wasan gasar Europa tsakaninsu da FC Utrecht.

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya ajiye kaptin din ya huta ne sannan kuma ba a saka Daniel Agger cikin jerin ba.

Amma dai an saka Fernando Torres wanda ya ci kwallo daya tal a kakar wasa ta bana cikin jerin 'yan wasa ashirin din da suka tafi Holland.

'Yan kwallon Liverpool Paul Konchesky da Fabio Aurelio duk ba zasu taka leda ba amma dai Dirk Kuyt zai kara da tsohuwar kungiyarshi.

A wasanta na farko Liverpool ta doke Steaua Bucharest daci hudu da daya a filin Anfield a ranar 16 ga watan Satumba.