Afrika ta Kudu na son ta dauki bakuncin gasar Afrika a 2015

Socer City
Image caption Filin wasa na Soccer City lokacin bukin rufe gasar cin kofin duniya

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Afrika ta Kudu SAFA ta tabbatar da cewa kasar na neman daukar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a shekara ta 2015.

Kasar na shirin kara wasu ginen ginen akan abubuwan da take dasu wadanda ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya.

A baya dai, Afrika ta Kudun ta dauki bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a 1996 inda kuma ta lashe gasar.

Shugaban Safa Cif Kirsten Nematandani ya ce "mun riga mun mika bukatar mu ga hukumar kwallon Afrika (caf)".

Abinda hakan ke nufi shine Afrika ta Kudu ta bi sawun Morocco wacce ta bayyana cewar tanason daukar bakuncin gasar ko a shekara ta 2015 ko kuma a 2017.

Za a gasar cin kofin Afrika ne a nan gaba a kasashen Gabon da Equatorial Guinea a shekara ta 2012, a yayinda Libya za ta daukin bakuncin na 2013.